Friday, December 5
Shadow

Shugaban kasa, Tinubu ya gana da sarkin Musulmi

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi Sa’ad Abubaka III a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja yayin da barazanar Trump ta kai hari ƙasar ke ci gaba da jan hankali.

Ganawar tasu na zuwa ne bayan Tinubu ya gana da Archbishop na Abuja Ignatius Kaigama.

Fadar shugaban ba ta bayyana abin da suka tattauna ba, amma ana sa ran ba za ta wuce yunƙurin kwantar da hankali ba yayin da wasu ke yaɗa iƙirarin yi wa mabiya addinin Kirista kisan ƙare-dangi.

Daga baya sarkin ya bi sawun shugaban ƙasar wajen yin sallar Juma’a a fadar shugaban ƙasa

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: A karshe dai Hisbah ta lalata wajen da aka ce wai an ga Sahun Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) a Kano mutane suka rika zuwa suna shan ruwan wajan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *