Tuesday, May 19
Shadow

Kundin Tarihin Duniya ya baiwa ‘Yar Najeriya, Hilda Baci shaidar shiga tarihin Duniya bayan data dafa shinkafa Dafaduka a Tukunya mafi girma a Duniya

Kundin bajinta na ‘Guinness World Records’ ya karrama matashiyar nan yar Najeriya Hilda Baci saboda girka dafa-dukar shinkafa mafi yawa a duniya.

A watan Satumban da ya gabata ne matashiyar ta yi wani gagarumin aikin girka dafa-dukar shinkafa mafi yawa cikin tukunya ɗaya a duniya.

Dafa-dukar shinkafa da ake yi wa laƙabi da ‘jollof’ abinci ne da ya shahara a ƙasashen Najeriya da Ghana da Senegal da Saliyo da Laberiya da ma wasu da dama.

Hilda mai shekara 28 a duniya ta yi shuhura ne a shekara ta 2023 bayan kafa tarihin kwashe lokaci mafi tsawo tana girki ita kaɗai, na tsawon sa’a 93 da minti 11

Karanta Wannan  An sake dawukye Dalibai a jihar Naija, Gwamnatin jihar Naija ta tabbatar da hakan saidai tace laifin hukumomin makarantar ne dan Gwamnati ta samu Rahoton hakan zai iya faruwa tace a kulle makarantu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *