Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin DIG Hashimu Argungu (Mai Ritaya) a matsayin sabon shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC).
Shugaban ya kuma amince da nadin Cif Onyemuche Nnamani a matsayin Sakatare da DIG Taiwo Lakanu (mai ritaya) a matsayin mamba a hukumar.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin Solomon Arase a matsayin shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC).
Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasar, shi ne wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce DIG Hashimu Argungu (Mai ritaya) ne sabon shugaban hukumar.
Majalisar dattawa za ta tabbatar da nadin.
Za a nada sauran mambobin hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda a kan lokaci, inji Ngelale.
Bugu da kari, shugaban kasar ya amince da nadin Mr. Mohammed Sheidu a matsayin babban sakataren hukumar kula da ‘yan sandan Najeriya NPTF da gaggawa.
Shugaban na fatan samun cikakkiyar nuna gaskiya, himma, da kishin kasa wajen gudanar da wadannan muhimman ayyuka don ci gaban rayuwar ‘yan sandan Najeriya da kasa baki daya.
Daga: Abbas Yakubu Yaura