Tuesday, January 7
Shadow

Shugaban Najeriya, Tinubu ya shiga jerin shuwagabannin kasashen Duniya mafiya rashawa da cin hanci inda ya zo a matsayi na 3

Wani rahoto da ya bayyana, ya nuna shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaba Mafi rashawa da cin hanci inda ya zo a matsayi na 3 a Duniya.

Wata kungiya me suna, (OCCRP) ce ta bayyana hakan.

Ta kuma samu wanna sakamako ne bayan da ta nemi a yi zabe dan fitar da mutane mafiya rashawa a Duniya.

Kungiyar ta hada da manyan ‘yan Jarida ne da ‘yan fafutuka dan kare hakkin al’umma. Shugban kasar Kenya, William Ruto ne ya zo na daya sai kuma shugaban kasar Indonesia, Joko Widodo ya zo na uku.

Hambararren Shugaban kasar Syria, Bashar al-Assad ne ya zamo gwarzon shekara.

Karanta Wannan  Allah Ya Yiwa Alhaji Ali Obobo Da Ya Taba Zuwa Ƙasar Saudiyya Kan Keke Rásųwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *