
Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin cewa, daga yanzu kar dansandan daya sake rike Bindiga indai yana sanye da kayan gida.
Ya kuma gargadi ‘yansandan su kiyaye kada su rika take hakkin dan Adam dan kuwa aikinsu shine kare hakkokin al’umma.
Ya bayyana hakane a yayin wani taro da aka yi a jiya inda yace ya samu korafe-korafe da yawa game da take hakkokin al’umma da wasu ‘yansandan ke yi.
Sannan Shugaban ‘yansandan yace duk wanda aka kama da karya wadannan dokoki zai dandana kudarsa.
Ya bukaci ‘yansandan su gudanar da aikinsu bisa doka dan kare mutuncin hukumar ta ‘yansanda.