Wednesday, January 15
Shadow

Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna

Sojojin Najeriya sun sun ce sun kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan arewa maso yammacin ƙasar mai suna Kachalla Buhari Alhaji Halidu da aka fi sani da Buharin Yadi da wasu yaransa fiye da 30..

Cikin wata sanarwa kwamishin harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar ya ce lamarin ya faru ne sakamakon wani gagarumin farmaki da dakarun rundunar ‘Sector 6 Operation Whirl Punch’ suka kai a kan iyakar Kaduna da Katsina

Ya ƙara da cewa Manjo Janar MLD Saraso ya jagoranci farmaki kan Yadi da mayaƙansa bayan samun rahotannin sirri da sojojin suka samu daga jihar Katsina.

Karanta Wannan  Muhammad Sanusi II ya goyi bayan zalunci a Kaduna>>Inji Shehu Sani

Sanarwar ta ce sojojin sun yi ba-ta-kashi da ‘yan bindigar a kusa da dajin Idasu, inda suka kashe ‘yan bindiga aƙalla 36 ciki har da Kacahalla Buharin Yadi.

Ƙasurgumin ɗan bindigar ya yi ƙaurin suna wajen kai hare-haren satar shanu da safarar makamai, da tashe-tashen hankula a jihohin arewacin ƙasar da dama.

Haka kuma rahotonni sun ce Buharin Yadi na da alaƙa da ƙungiyoyin ‘yan bindiga a yankin arewa maso gabashi da arewa masi yammacin ƙasar.

Sanarwar ta ce sojoji sun kwashe fiye da shekarar biyar suna ɗan bindigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *