YANZU-YANZU: Sojojin Nijeriya Sun Yi Haďari A Kan Dutsen Mambilla, Dake Jihar Taraba.

Sojoji huɗu sun jikkata a wani haɗarin mota da ya afku a Dutsen Mambilla da ke jihar Taraba. Lamarin ya faru ne a yayin da dakarun ke tsaka da tafiya a cikin tsaunukan yankin.
Mai Martaba Dr. Shehu Audu Baju, Sarkin Mambilla, ya nuna ƙwarin gwiwa da tausayinsa ta hanyar sa hannu a ceto sojojin da suka samu rauni. Bayan an ceto su, an garzaya da su Barikin Sojoji na 20 Battalion da ke Serti domin samun kulawar gaggawa.
Muna addu’ar Allah Ya ba su lafiya, Ya kuma kare sauran jami’an tsaro da ke bakin aiki.