Wednesday, March 18
Shadow

Suma ‘yan Kwallon Kwando mata Shugaba Tinubu ya baiwa kowaccensu kyautar Naira Miliyan 150 da gidaje

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ba ƴan wasan kwandon Najeriya mata dala 100,000 da lambar girma ta OON saboda nasarar da suka samu ta lashe kofin gasar kofin Afirka ta wato Afrobasket.

Shugaban ya kuma ba masu horar da ƴanwasan dala 50,000 kowannensu.

hakanan kowannensu an bata kyautar gida hadda masu horas dasu.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a madadin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugaban ya ƴanwasan ƙwallon ƙafa mata kyautar dala 100,000 da lambar girma.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon da Duminsa: Yanda Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, FCDA karkashin Wike ta kutsa da karfi cikin Ginin River Park duk da Umarnin Kotu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *