Sunday, April 5
Shadow

Sun bashi gida, da Mota da jami’an tsaro sosai, yana tafiya kamar wani Gwamna>>Atiku Abubakar yayi magana akan Nafiu Bala Gombe da ya kaisu Kotu yace shine Shugaban ADC na gaskiya

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, Masu daukar nauyin Nafiu Bala Gombe da ya kaisu kotu yace shine shugaban APC na gaskiya sun bashi gida sun bashi mota sannan sun bashi jami’an tsaro sosai yana tafiya kamar wani Gwamna.

Atiku ya bayyana hakane a hirar da DWHausa suka yi dashi.

Duk da dai bai kira sunan Nafiu Bala Gombe ba amma da yawa sun fassara cewa Atiku dashi yake.

Atiku yace anawa ADC wannan zagon kasar ne saboda karbuwar data samu a hannun al’ummar Najeriya.

Saidai yace hakan bai hana mutane na ta kara yin tururuwa zuwa cikin jam’iyyar ba.

Karanta Wannan  Mutane 9 sun rasu sanadiyyar hadarin mota a jihar Jigawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *