Babu tsayayyar magana akan ainahin sunan Fir’auna wanda suka yi zamani da Annabi Musa (A.S).
A Qur’ani dai an bayyana mana sunansa da fir’auna, saidai masana tairihi na zamani, sun bayyana cewa, sunan Fir’auna, sunan sarautane a kasar Misra/Egypt, akwai ainahin sunansa na gaskiya.
Majiyoyi da yawa sunce sunan Fir’auna na gaskiya shine MUSAB BIN WALID.
A turance kuma, Masana Tarihi da yawa sun ce sunan sa, Ramesses II Saidai wasu kalilan sun ce sunansa Seti I.
Ko ma dai menene sunansa, abin sani shine la’anannen Allah ne, wanda yayi mulki da zalunci wanda kuma karshensa wuta.
Allah ne mafi sani.