
Fadar shugaban kasa, ta tabbatar da cewa, ministan Kudi, Wale Edun Bashi da lafiya
Wata majiya daga fadar ta tabbatar wa da gidan jaridar Punchng hakan inda tace rashin lafiyar ta matsa masa.
Saidai tace ba Shanyewar rabin jiki bane sannan ba’a fitar dashi zuwa kasar waje ba, sannan shugaban kasa Bola Tinubu bai fara neman wanda zai maye gurbinsa ba.
Rahotanni sun ce Likitocin Najeriya ne ke kula da Ministan amma idan lamarin yayi kamari za’a iya fita dashi kasar waje.