Friday, December 5
Shadow

Tambuwal ya zargi APC da kawo rashin jituwa a cikin jam’iyyun Adawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya zargi shugaban Najeriya Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki da dagula lamuran jam’iyyun hamayya a ƙasar.

Yayin wata hira da gidan Talbijin na Channels a ranar Juma’a, tsohon kakakin majalisar wakilan ƙasar, ya yi iƙirarin cewa da gangan Tinubu ke kitsa rikicn da jam’iyyun hamayya ke ciki.

Ɗanmajalisar dattawan – wanda ke cikin jam’iyyar ADC ta masu haɗaka – ya ce idan aka yi la’akari da abubuwan da ke faruwa a jam’iyyun hamayya a yanzu za a fahimci cewa da wata a ƙasa.

”Ba sai an faɗa maka ba, duk musan da kowa zai yi ciki kuwa har da Shugaba Bola Tinubu, cewa ba shi da hannu na ƙoƙarin ruguza jam’iyyun hamayya, ba gaskiya ba ne”, in Tambuwal.

Karanta Wannan  Mace ta Gari: Mijina Ya Taba Hana Ni Zuwa Umarah A Lokacin Bai Fi Awanni Hudu Ya Rage Mu Tashi Ba, Amma Saboda Kauna Da Biyayya Haka Na Hakura, Inji Bahijja Kabara

Tsohon gwamnan na Sokoto ya ce ”ba zargi nake yi ba, suna da hannu a duka abubuwan da ke faruwa a jam’iyyun hamayya”.

A baya-bayan nan dai an ga yadda manyan jam’iyyun hamayyar ƙasar suka faɗa rikicin cikin gida, wani abu da masana ke gargaɗin zai jonyo musu mummunan koma-baya.

Tuni dai wasu ƴaƴan jam’iyyun hamayyar cikin kuwa har da gwamnoni da ƴan majalisar dokokin ƙasar suka fice daga jam’iyyun nasu tare da komawa APC mai mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *