
Tauraron mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa, Ko shi ya tsaya takarar shugaban kasa, sai ya kayar da su Atiku da El-Rufai.
Ya bayyana hakane a ganawarsa da kafar DLCHausa.
Rarara yace Dan haka hadakar ‘yan siyasar adawar ba zasu iya kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba.
Yace shi yafi su Atiku abinda zai fada yayi na taimakon Al’umma a zabeshi ballantana Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Rarara dai shine babban mawakin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.