Tashin Hankali: Wata Amarya ta yiwa Ango yankan rago a Kano kwana 9 da aurensu.

Rahotannin da ke shigo wa Jaridar Arewa yanzu haka sun tabbatar da cewa ana zargin wata amarya da yiwa Angonta yankan rago a daren jiya Litinin, a jihar Kano.
Lamarin ya faru a unguwar Farawa da ke cikin birnin Kano. Bayanai sun tabbatar da cewa Amaryar ta fara shayar da shi guba ne a Lemu, daga bisani ta yi masa yankan rago kamar yadda ta Dala FM ta ruwaito.
Hakazalika wani rahoton ya ce an yi masu auren zumunci ne a ranar 27 ga watan Afrilu, wanda yau kimanin kwana 9 kenan.
Zuwa yanzu jami’an tsaron yan sanda sun samu nasarar kama Amaryar domin bincike.
- Jaridar Arewa