Tuesday, September 22
Shadow

Ba da yawuna aka kafa allon da ke nuna ‘Katsina babu ƙorafi’ ba a Katsina ~ Dikko Raɗɗa

Ba da yawuna aka kafa allon da ke nuna ‘Katsina babu ƙorafi’ ba a Katsina ~ Dikko Raɗɗa.

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa yace a matsayinsa na gwamna, bai da masaniya dangane da kafa wani allo da ke nuna cewa Al’ummar Jihar ba su da ƙorafi bisa ga salon Mulkin shugaba Tinubu ba.

Hasalima Gwamnan yace, sun gabatar ma shugaba Tinubu ƙwararan ƙorafe-ƙorafe har guda 3 da ke buƙatar a magance masu, wanda suka haɗa da Matsalar tsaro, kammala wuta mai amfani da hasken Rana, da kuma fadada filin sauka da tashin jirage na Umar Musa Yar’adua da ke Katsina.

Bayan haka ya ja hankalin masu suka da su riƙa tantance labarin da suka gani a kafafen sada zumunta domin tabbatar da asalin labarin, kafin sukar wanda baya da masaniya a kai.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Nakan Buga Misali da maganganun babban Malami Ibn Taimiyya duk da wasu daga cikin 'yan Dariqarmu basa son ina hakan>>Inji Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari

Daga Lukman Aliyu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *