
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ba da umarnin kammala aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kano cikin wata 12.
Mai magana da yawun fadar shugaban Najeriya, Sunday Dare, ya ce a yau Litinin shugaban ya amince bayar da umarnin.
“Shugaba Tinubu ya amince da kasafin kammala wuraren da ba a gama ba a kan titin Abuja-Kaduna, da na Kaduna-Zaria cikin wata 12,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na dandalin X.
Ya ƙara da cewa “wannan titi ne mai muhimmanci ne a kodayaushe”.
A watan Janairu gwamnatin Bola Tinubu ta sanar da bai wa wani sabon kamfani ƙarashen aikin titin bayan ta ƙwace kwangilarsa daga hannun Julius Berger.