Friday, July 17
Shadow

Babban Dansandan Najeriya da aka yi Gàrkùwà dashi a Abuja ya kubuta

Rundunar ‘yansandan Najeriya a Abuja babban birnin Najeriya ta ce jami’inta da aka bayar da rahotonnin cewa an sace ya koma gida tuni.

Da take tabbatar wa da BBC ta wayar tarho, kakakin rundunar Josephine Addeh ta ce da ma ba wani mummunan abu ne ya faru da Sufuritanda Modestus Ojiebe ba.

“Motarsa ce ta samu matsala kawai a kan hanya, kuma gaba ɗaya abin da ya faru bai fi ‘yan awanni ba ya kuɓuta kuma ya koma gida,” in ji ta.

Tun da farko was kafofin yaɗa labarai sun ruwaito cewa motar ɗansandan ce ta samu matsala a kan babban titin Abuja zuwa Kaduna, inda wasu da ake zargin masu garkuwa ne suka yi awon gaba da shi.

Karanta Wannan  Mun samar da tsaro sosai a Yankin Arewa, yanzu mutanen da a baya suka tsere daga gidajensu, sun koma garuruwansu>>Inji Shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *