Friday, December 5
Shadow

Tinubu ya bai wa mutanen Mokwa tallafin naira biliyan biyu da shinkafa tirela 20

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya ce shugaban ƙasar Bola Tinubu ya amince da bai wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Neja gudumawar kuɗi naira biliyan biyu da kuma tirela 20 na shinkafa.

Shettima ya sanar da hakan ne a garin Mokwa, lokacin ziyarar da ya kai bayan ambaliyar ruwa da ta ɗaiɗaita garin wadda ta lalata dukiya da kadarori da kuma sanadiyyar salwantar ɗaruruwan rayuka.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce za a magance duk wasu matsaloli da ke addabar al’ummar.

Inda ya ce shugaban ƙasar ya bayar da umarnin gyara gadojin da ambaliyar ta lalata ba tare da ɓata lokaci ba.

Karanta Wannan  Za'a kori Peter Obi daga jam'iyyar Labour Party saboda ya shiga hadakar 'yan Adawa ta kayar da Tinubu

Hukumomi sun tabbatar da mutuwar sama da mutum 200 a ambaliyar ta ƙaramar hukumar Makwa da ke jihar Neja a arewa ta tsakiyar Najeriya.

Haka nan akwai sama da mutum 500 da ba a san inda suke ba, wani abu da ake fargabar zai ƙara yawan mutanen da suka rasa rayukansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *