Thursday, October 15
Shadow

An yanke wa limamin masallaci shekaru 5 a gidan yari sakamakon kàshè alade

Wata kotu a Rwanda ta ɗaure wani malamin addinin Islama har na tsawon shekara biyar a kurkuku sabo da ya kashe wani alade a harabar wani masallaci.

Wasu shaidu uku sun shaida wa kotun cewa sun ga limamin mai suna Sadate Musengimana yana dukan aladen da wani katako matakin da ya kashe shi nan take.

Sai dai lauyansa ya shaida wa kotun cewa ba da gangar ya kashe aladen ba, yana cewa ya yi kokarin koran shi daga harabar wani masallaci da ke gundumar Kayonzo a gabashin kasar ne cikin watan Fabrairu.

“Da yaji yara na cewa wani alade ya shiga masallacin, sai ya fito da wata sanda domin ya kore shi. Ya daki aladen kuma ya mutu, amma bai yi niyyar kashe shi ba,” kamar yadda lauyansa Yusuf Nsengiyumva ya shaida wa BBC.

Karanta Wannan  A shekarar da 2023, 'Yar Arewa, Aisha Abubakar ta shiga gasar Sarauniyar Kyau ta Najeriya sanye da kaya masu dan mutunci, saidai bata ci ba, A shekarar 2025 ta cire kayan mutunci inda ta shiga gasar da kaya masu nuna tsyrayci, saidai a wannan karin ma bata ci ba

Lauyan ya ce ya daukaka kara kan wannan hukuncin “mai tsanani”.

Tun watan Fabrairu ake tsare da Liman Musengimana, watan da ya kashe aladen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *