
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nemi tawagar ƙwallon ƙafa ta matan ƙasar da ta kai masa kofin gasar ƙasashen Afirka yayin da suke shirin buga wasan ƙarshe a yau Asabar.
Najeriya za ta kara da mai msaukin baƙi Morocco a birnin Rabat domin neman lashe kofin a karo na 10 jimilla, yayin da Moroccon ke neman kofin a karon farko.
“A madadin ƙasar nan baki ɗaya, muna goyon bayanku tare da yin addu’ar ku yi nasara a daren yau, yayin da kuke neman kafa tarihin cin kofi na 10,” a cewar Tinubu cikin sanarwar da fadar shugaban ta fitar.