Tinubu ya naɗa sabon shugaban gidan talabijin na ƙasa, NTA

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi babban sauy-sauye na shugabanci a gidan talabijin na ƙasa, NTA, inda ya naɗa Rotimi Richard Pedro, a matsayin sabon Darakta-Janar na gidan talabijin din na gwamnati.
“Sauran manyan nade-naden sun haɗa da Karimah Bello daga Jihar Katsina a matsayin Daraktar Tallace-Tallace, Stella Din daga Jihar Filato a matsayin Daraktar Labarai, da kuma Sophia Issa Mohammed daga Jihar Adamawa a matsayin Babbar Darakta ta Kamfanin NTA Enterprises Limited.
“Pedro, ɗan asalin Legas, fitaccen mai kasuwanci a fannin kafafen watsa labarai da kuma mai ba da shawara, wanda ke da kusan shekaru talatin na kwarewar jagoranci a harkar watsa shirye-shirye, wasanni, da kuma tallace-tallace a faɗin Afirka, Birtaniya da Gabas ta Tsakiya,” in ji sanarwar.