
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Ismael Ahmed, tsohon hadimin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, a matsayin Shugaban Hukumar Presidential Compressed Natural Gas Initiative (PCNGi). Wannan shiri na gwamnati na da nufin rage radadin cire tallafin fetur ta hanyar samar da makamashi mai araha da tsafta.
Ismael Ahmed ya kasance mai ba Buhari shawara kan Shirin Tallafin Jama’a tsakanin 2018 zuwa 2022. Ya kammala karatunsa na lauya a Jami’ar Abuja, sannan ya samu digirin digirgir a fannin Hulɗar Ƙasashen Duniya daga Jami’ar Webster da ke Amurka.