Friday, January 16
Shadow

Tinubu zai je Afirka ta Kudu da Angola

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai bar ƙasar a yau Laraba domin halartar taron G20 da taro tsakanin kungiyar Tarayyar Turai da ta Tarayyar Afirka.

‎Shugaban zai soma ziyarar ne a Johannesburg,babban birnin ƙasar Afrika ta kudu, inda zai halarci karo na ashirin na taron shugabannin ƙasashe ashirin masu ƙarfin tattalin arziƙi wato G20 a ranakun 22 da 23 ga watan Nuwamba.

Daga nan zai tafi birnin Luanda da ke Angola domin halartar taron kungiyar Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka karo na 7 a ranakun 24 da 25 ga watan Nuwamban 2025.

Waɗannan bayanai na ƙunshe ne a cikin sanarwa da mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga ya fitar a babban birnin ƙasar Abuja, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Karanta Wannan  Me zai faru da shari'o'in da ake yi wa Trump bayan ya lashe zaɓe?

Ana kuma sa ran Shugaba Tinubu zai yi wasu ganawa a yayin taron domin bunkasa shirinsa na sabunta fata da kuma tattaunawa kan zaman lafiya da tsaro da kuma ci gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *