
Shugaba Bola Tinubu zai bar Abuja a gobe Asabar domin ziyarar ƙasashe biyu Saint Lucia da Brazil, kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa, Bayo Onanuga ta bayyana.
Sanarwar ta ce da farko shugaban zai yada zango a Saint Lucia a ziyarar da zai yi domin kyautata dangantaka tsakanin Najeriya da ƙasashen yankin Karebiya.
Daga nan kuma shugaban zai tashi ya nufi Brazil domin halartar taron ƙoli na 17 na ƙungiyar ƙasashe masu haɓakar tattalin arziƙi ta BRICS a birnin Rio de Janeiro, daga ranar 6 – 7, ga watan Yuli mai kamawa, 2025.
Zai halarci taron ne a matsayin Najeriya na abokiyar tafiyar ƙungiyar.
Afirka ta Kudu da Masar da Habasha su ne ƙasashen Afirka da ke zaman mambobin ƙungiyar a Afirka.