
Tauraruwar Tiktok me sayar da kayan mata wadda Abokin sana’arta, Shahararren Tiktok, Gfresh Al-amin Yaso ya aura a kwanakin baya amma ya fasa, watau Alpha Charles Borno, ta yi masa tonon silili.
A wani Live da Alpha Charles Borno ta yi, tace Gfresh ya nemi yin lalata da ita kamin su yi aure amma ta kiya.
Tace sun je daga Kaduna suka sauka a Kano sai ta cewa wadda suka je tare ko Gfresh ya je ya ce ta fita daga dakin kada ta fita.
Haka kuwa aka yi Alpha Charles Borno tana bacci sai ga Gfresh, sai ya cewa wadda suke tare da Alpha din ta fita ta basu guri mata da miji zasu yi magana.
Sai ta kiya, yayi iya yinsa amma taki, daga nan ne sai ya fita ya fara Bidiyo yana cewa aurensu ya samu matsala.
Alpha Charles Borno ta bayyana cewa duk tana da hujjojinta akan abinda take fada.