
Tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun ya bayyana cewa, Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya fi shekaru 88 kamar yanda yake ikirari.
Yace shekarun tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo sun kai tsakanin 93 ko 94.
Ya bayyana hakane yayin da ake bikin cikar tsohon shugaban kasar shekaru 88.
Saidai tsohon shugaban kasar yace ba gaskiya bane, shekarunsa 88 kamar yanda suke a hukumance.