Kungiyar masu hada magunguna ta koka da cewa tsadar rayuwa tasa yanzu mutane da yawa basa iya sayen magunguna.
Kungiyar ta alakanta hakan da tashin farashin magunguna da kayan hadasu da karyewar farashin dala da dogaro da shigo da kayan hada magunguna da shigo da magungunan daga kasashen waje.
Kungiyar ta bayyana hakane a wajan wani taro da aka yi a A Legas na masu ruwa da tsaki a cikinta.