Tsaffin sojoji da suka yi ritaya ranar Talata sun kai kujeru da rumfa a kofar fishin ma’ikatar kudi dake Abuja inda suka yi zaman dirshan suka bukaci a biyasu hakkokinsu.
Dama dai a watan Disamba daya gabata, sojojin sun yi irin wannan zanga-zanga ta neman hakkinsu.
Watanni da yawa sun shude inda ake gayawa tsaffin sojojin cewa, babu kudin da za’a biyasu hakkokin nasu.
Bayan zanga-zangar da suka yi a watan Disamba, an biyasu kaso 50 cikin 100 na hakkokin nasu inda aka musu alkawarin biyan suran amma sunce har yanzu shiru.