Sunday, April 26
Shadow

Tsaffin sojoji da suka yi ritaya sun yi zanga-zangar rashin biyansu albashi

Tsaffin sojoji da suka yi ritaya ranar Talata sun kai kujeru da rumfa a kofar fishin ma’ikatar kudi dake Abuja inda suka yi zaman dirshan suka bukaci a biyasu hakkokinsu.

Dama dai a watan Disamba daya gabata, sojojin sun yi irin wannan zanga-zanga ta neman hakkinsu.

Watanni da yawa sun shude inda ake gayawa tsaffin sojojin cewa, babu kudin da za’a biyasu hakkokin nasu.

Bayan zanga-zangar da suka yi a watan Disamba, an biyasu kaso 50 cikin 100 na hakkokin nasu inda aka musu alkawarin biyan suran amma sunce har yanzu shiru.

Karanta Wannan  Sanatoci sun ce in rokeka a sake duba janye musu jami'an tsaron 'yansanda da aka yi, dan basu iya komawa garuruwansu haka ba jami'an tsaro>>Sanata Godswill Akpabio ya gayawa shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *