Rahotanni na cewa an samu mutuwar mutane da dama sakamakon tsananin zafi a Indiya. Hukumomin jihohin gabashin ƙasar, Odisha da Bihar sun ce mutane 15 ne suka rasu a ranar Alhamis, kuma suna ci gaba da bincike kan lamarin.
An haramtawa ma’aikata zirga-zirga a tsakiyar rana.
Ana hasashen cewa za a ci gaba da fuskantar tsananin zafi a gabashi yayin da ake hasashen za a samu sauƙin zafin a Arewa maso Yamma da kuma tsakiyar Indiya.