
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu tabbaci cewa, ba sai ya je yakin neman zabe ba jihar Kogi.
Yace shugaban ne zai yi nasara a zaben shekarar 2027 me zuwa.
Ya bayyana hakane a wajan yakin neman zabe inda ake nuna goyon bayan ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da kuma gwamna Usman Ododo na jihar kan su zarce a karo na biyu.