
Tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya kawo Tauraron kwallon kafa, Cristiano Ronaldo da sauran ‘yan kwallon kasar Portugal Najeriya su yi wasa.
A cewarsa, hakan zai taimaka matuka wajan farantawa ‘yan Najeriya rai musamman kamin zaben shekarar 2027.
Malam Bashir yace dalilinsa shine mafi yawan ‘yan Najeriya masoya Cristiano Ronaldo ne.
Malam Bashir yayi wannan maganane bayan da Kasar Ghana ta kawo Messi da sauran ‘yan wasan kasar Argentina kasar suka buga wasa akan dala Miliyan $12.