Monday, April 14
Shadow

Tun farko gayyatar da shelkwatar ƴansanda ta yi wa Sarki Sanusi ba ta da amfani – Peter Obi

Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP), ya yaba wa Rundunar ‘Yansandan Najeriya bisa janye gayyatar da ta aikewa Muhammadu Sanusi, Sarkin Kano.

A makon da ya gabata ne, ‘yansanda suka gayyaci Sanusi zuwa hedikwatar rundunar domin yi masa tambayoyi kan zargin kashe-kashe da suka faru a lokacin bikin Eid-el-Fitr da ya gabata.

Da yake mayar da martani a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, Obi ya ce hanyar warware matsalar a matakin ƙasa-ƙasa (wato ba tare da tursasawa daga sama ba) zai ƙara kawo zaman lafiya da amincewar jama’a.

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce ba bu buƙatar wannan gayyata tun da farko, kuma hakan na iya tayar da hankali a lamarin da tuni ya ɗauki zafi.

Karanta Wannan  An yankewa malamin jami'a hukuncin daurin rai da rai bayan samunsa da yiwa dalibarsa Fyàdè

“Ina so in yaba wa Rundunar ‘Yansandan Najeriya saboda wannan hukuncin da ta ɗauka cikin hikima a kan lokaci, na janye gayyatar da aka aikewa Mai Martaba Muhammadu Sanusi II,” in ji Obi.

“Idan aka yi la’akari da yanayin tashin hankali a cikin al’umma a yanzu, irin wannan gayyata ba ta da wani amfani, kuma tana iya ƙara tayar da hankali a cikin rikicin da tuni ya yi zafi.

“Akwai cikakkiyar rundunar ‘yan sanda mai aiki a jihar Kano, wadda ke da ƙwarewa da ƙarfin da za ta iya magance irin waɗannan lamurra a cikin jihar.

“Shi ya sa muke da manyan jami’ai masu matsayi irin su Kwamishinonin ‘Yan Sanda da Mataimakan Sufeto Janar na Shiyya (AIGs), domin su rika gudanar da irin waɗannan al’amura a matakin jihohi da shiyyoyi.”

Karanta Wannan  Hotuna da Bidiyo: Kalli Kananan yara da aka barsu da yunwa bayan kamasu saboda sun yiwa gwamnatin Tinubu zanga-zanga, wasu daga cikinsu sun fadi ana tsaka da musu shari'a saboda yunwa, An bayar da belinsu akan Naira Miliyan 10 kowanne yaro daya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *