Friday, March 14
Shadow

Uba Sani da Nuhu Ribadu ba abokaina ba ne yanzu – El-Rufa’i

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa ‘a yanzu Uba Sani ba abokinsa ba ne’ bayan abubuwan da ke faruwa baya-bayan nan.

El-Rufa’i ya bayyana hakan ne a tattaunawar da ya gudanar da tashar talabijin ta Arise da yammacin yau Litinin.

Bayan kammala wa’adinsa na shekara takwas a matsayin gwamnan jihar Kaduna, tsohon gwamnan na fuskantar bincike kan kuɗaɗe da ake zargin sun yi ɓatan-dabo a lokacin mulkinsa.

Lamarin ya haifar da muhawara kasancewar thonon gwamnan na Kaduna, Nasir El-Rufa’i da gwamna mai ci Uba Sani sun kasance masu kusanci a tsawon shekara takwas na mulkin tsohon gwamnan.

El-Rufa’i ya bayyana cewa aboki shi ne mutumin da zai kawo maka ɗauki ko a lokacin daɗi ko na tsanani.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna: An kama 'yar kasar Thailand da ta shigo da muggan kwàyòyì Najeriya

Ya ce “a yanzu Uba Sani da Nuhu Ribadu ba abokaina ba ne.

“Na san cewa abokaina sun san cewa zan iya kai musu ɗauki a kowane lokaci,” in ji tsohon gwamnan.

A game da zargin da ake yi masa, El-Rufa’i ya ce bai taɓa cin ko sisi na kuɗaden da ba nashi ba a muƙaman da ya riƙe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *