Sunday, January 11
Shadow

Venezuela ta zargi Amurka da sata da kuma fashin teku

Venezuela ta zargi Amurka da sata karara da kuma fashin teku bayan da dakarun Amurkan suka kwace wani jirgin ruwa na dakon mai a gabar tekun Venezuela din.

Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce matakin wani shiri ne na lalata arzikin makamashi na Venezuela da gangan.

Sai dai jami’an Amurka sun ce jirgin ruwan yana safarar man da aka sanya takunkumin sayar da shi ne zuwa Iran kuma kudin da ake samu daga cinkin ana taimaka wa kungiyoyin ta’addanci ne.

Lamarin ya kasance ƙarin wata sabuwar dambarwa ta matsin lambar da Amurka ke yi wa shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro – mai ra’ayin gurguzu.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Ji Matakin da aka dauka kan Sheikh Abduljabbar Bayan zaman Kwamitin Shura da Malam Lawal Triumph

Mai dai shi ne babbar hanyar samun kudade na kasar ta Venezuela

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *