Wednesday, January 15
Shadow

Wacece mace mai addini

Mace mai addini itace kamila wadda ke da kamun kai, da ilimi na addini dana boko, wadda kuma ta samu tarbiyya irin ta addinin musulunci.

Mace mai addini itace wadda bata shigar banza dake nuna tsiraicinta, gashinta a rufe, ba ta sa matsatstsun kaya, bata sa kaya shara-shara Wanda ke nuna cikin jikinta, ta na son saka hijabi.

Mace mai addini idan tana da saurayi bata zama kusa dashi su manne suna jin dumin jikin juna. Kuma duk son da take masa bata yadda ya taba jikinta.

Mace mai addini tana kokarin kiyaye dokokin Allah da kuma tunatar da Wanda suke kusa da ita suma su kiyaye dokokin Allah.

Karanta Wannan  KARANTA KA KARU: Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hajji

Mace me addini ta iya kalamai na hankali Wanda babu wauta, cin fuska, ko wulakanci a ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *