WANI DAN JAGALIYA YA CHAKAWA NI BABBAN SOJA WUKA HAR LAHIRA A GADAR KAWO TA JIHAR KADUNA.

Rahotanni daga Jihar Kaduna sun tabbatar da cewar Wani babban jami’in soja, Laftanar Commodore M. Buba, ya rasa ransa bayan da wani ɓarawon waya ya soka masa wuƙa a ƙirji, Kuma ya rasa rayuwar sa har Lahira.
Bala’in ya faru ne a gadar Kawo, lokacin da jami’in ya tsaya domin gyara tayar motarsa da ta fashe yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Jaji, inda yake karatu a Makarantar Horas da Sojoji ta Armed Forces Command and Staff College.
Kakakin hukumar Yan’sanda ta kasa reshen Jihar Kaduna DSP Mansur Hassan ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Shedun gani da Ido sun ce Sojan ya hana barawon wayar ne kamar yadda ya bukata tun da farko, shi Kuma barawon ya zare wuka ya soka masa a kirji.
Al’ummar gari sun farmaki barawon da duka har sai da suka yi ajalinsa.
Nan take suka garzaya da Sojan Asibitin Manal dake kawo don cetar rayuwar sa karshe sai dai gawar sa aka sauya wa ma’ajiya zuwa Asibitin Sojoji na 44 dake kwaryar Jihar Kaduna.
Jami’an tsaro daga hukumomi daban-daban sun fara binciken kwakwaf don kame tare da gurfanar da masu hannu a Wannan mugun aikin.