
Wani matashi mai shekaru 20 da ya amsa da bakin da cewa ya kashe mutane wajen ƙwacen waya a gurare daban-daban ya miƙa kansa da kansa ga rundunar ‘yansanda ta jihar Kano.
Wanda ake zargin, wanda aka bayyana sunansa da Umar Auwal, mai lakabi da ‘Abba Dujal,’ mazaunin karamar hukumar Wudil a jihar Kano, ya amsa cewa yana da hannu a laifukan kisan kai, fashi da makami da kuma sata, musamman na babura da wayoyin hannu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, SP Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa miƙa kansa da Auwal ya yi ya biyo bayan zurfafa samame da rundunar ke yi a maboyar ‘yan ta’adda a jihar.
Kiyawa ya ce wannan mataki yana daga cikin kokarin da rundunar ke yi na dawo da doka da oda da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Auwal ya amsa cewa ya daba wa wani mutum da aka fi sani da ‘Boka’ wuka a unguwar Sabon Gari, Kano, sannan ya kwace masa wayarsa kirar Infinix Hot 40i, wadda daga baya ya saida da Naira 40,000.
Haka kuma ya amsa cewa ya kashe wani mutum a unguwar Kurna kuma ya sace wayarsa kirar Samsung S26, wadda ya sayar da ita da Naira 160,000.
A wani harin makamancin haka a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa, Auwal ya amsa cewa ya kashe wani mutum tare da sace babur dinsa wanda daga bisani ya saida da Naira 300,000.
Kiyawa ya kara da cewa ana tsare da wanda ake zargin a sashen binciken kisan kai na rundunar, inda jami’an bincike ke ci gaba da gudanar da zurfaffen bincike don tabbatar da gaskiyar ikirarin da ya yi da kuma gano yiwuwar wasu abokan aikata laifi da sauran laifuka da zai iya yi.