
Wani Bidiyo ya nuna cikin Cell din ‘Yansandan Najeriya da kuma yanda ake tsare da masu Laifi.
A Bidiyon an ga wani me laifi ko wanda ake zargine yake daukar Bidiyon da wayarsa.
Da yawa sun rika tambayar shin dama ana barin masu laifi su shiga dakin da ake tsaresu da waya?
Sannan wasu sun rika tambayar shin a ina suke fitsari da kashi, saboda ba’a ga bayi ba.