Tuesday, May 19
Shadow

Kalli Bidiyon: Minti Biyar kamin Amurka ta kai Khàrì Sokoto mun yi magana dasu mun amince musu>>Inji Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya tace Mintuna 5 kamin harin da Amurkar ta kai Sokoto, ta yi magana da Amurkar kuma a amince.

Ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar ne ya bayana hakan.

Yace yayi magana da jami’in hulda da kasashen waje na kasar Amurka, Marco Rubio inda yace masa suna neman izinin kawo hari Najeriya.

Sai yace masa zai nemi Izini wajan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, kuma shugaban kasar ya amince da kai harin.

Yace sun dade suna neman yin aiki tare da kasar Amurka dan magance matsalar tsaron Najeriya.

Karanta Wannan  Ina Son In Sanar Al'ummar Jihar Katsina Da Ku Cewar "Shugaban Kasa Bola Tinubu Zai Zo Jihar Katsina Kuma Ya Kwana, Wanda Bai Taɓa Yi Ba A Cikin Jihohin Najeriya, Bayan Mahaifarsa Jihar Legas, Domin Taya Mu Murna Da Kuma Ƙaddamar Da Ayyuka. Ina Kira Ga Al'ummar Jihar Katsina Su Fito Tarbar Shugaban Kasa".

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *