
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya bayyana cewa, Akwai wata kungiyar magoya bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da yake cikinta wadda suka ce ‘yan Arewa jahilaine.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace ya gaya musu cewa wannan mutane sune ake neman kuri’arsu.
Yace Salon Mulkin Tinubu bai yi masa ba inda yace da ace yana cikin gwamnatin Tinubu da tuni ko dai ya sauka daga mukaminsa ko an koreshi ko wani abun.