Friday, August 7
Shadow

Wasu magoya bayan Tinubu sun gaya min cewa ‘yan Arewa jahilaine>>Inji Babachir Lawal

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya bayyana cewa, Akwai wata kungiyar magoya bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da yake cikinta wadda suka ce ‘yan Arewa jahilaine.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace ya gaya musu cewa wannan mutane sune ake neman kuri’arsu.

Yace Salon Mulkin Tinubu bai yi masa ba inda yace da ace yana cikin gwamnatin Tinubu da tuni ko dai ya sauka daga mukaminsa ko an koreshi ko wani abun.

Karanta Wannan  Ba AI bane: Kalli hotunan Yanda aka ga wani abu me kama da surar mutum a sararin samaniyar kasar Greece, saidai masana Kimiyya sunce kada wanda ya tayar da hankalinsa, Tauraron dan Adam ne ya hasko Duniya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *