
Tun bayan da Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa ana kashe kiristoci da yawa a Najeriya ne da yawa ke ta sharhi da bayyana abinda suka fahimta game da lamarin.
Wasu sun bayyana cewa suna zargin ci gaban da matatar man Dangote ta dauko ne inda nan da wani Lokaci Dangoten yace zata zama ta daya a Duniya wajan yawan tace man Fetur da ganga Miliyan 1.4 a kullun shine ya hana Turawa sakat suke kokarin ganin sun Lalata kasar.
A gefe guda kuma wasu na ganin cewa Arzikin da Allah yawa Najeriya ne Turawan ke son zuwa su kwasa.
Wasu dai na cewa, zuwan Amurka Najeriya da sunan yakar ‘yan ta’adda ba abin Alheri bane musamman lura da irin yanda suka lalata kasashen Libya, Afghanistan, Syria da sauransu.