
Wasu ‘yan jam’iyyar ADC sun maka sabbin Shuwagabannin jam’iyyar da aka nada na kwanannan a kotu inda suke neman kotun data bayyana ko shugabancin nasu ya halasta a doka?
Wadanda suka kai karan su 4 ne da suka hada da Adeyemi Emmanuel, Ayodeji Victor Tolu, da Haruna Ismaila.
Sun nemi kotun ta kuma hana hukumar zabe me zaman kanta INEC ta amince da sabbin shuwagabannin na riko.
David Mark ne aka baiwa shugaban jam’iyyar na riko sai kuma Rauf Aregbesola aka bashi sakataren jam’iyyar na riko.