Thursday, January 15
Shadow

Wata Kungiyar masu ikirarin Jìhàdì ta je kusa da Abuja ta kafa sansani

Kungiyar dake ikirarin jìhàdì ta Ansaru ta je kusa da babban birnin tarayya Abuja ta kafa sansani.

Rahoton yace kungiyar wadda ta balle daga Bòkò Hàràm ta kuma kafa sansanoni 8 a cikin jihar Kogi.

Wasu daga cikin sansanonin kungiyar na tsakanin Obajana da Kabba wanda hakan yasa manyan mutane dake wucewa ta wajan biyan kudi masu yawa dan samarwa kansu tsaro yayin wucewa ta wajan.

Rahoton yace babban wajan horas da ‘yan kungiyar na kilomita 93 ne tsakaninsa da babban birnin tarayya, Abuja.

Kokarin jinn ta bakin hukumomin tsaro kan lamarin ya ci tura.

Karanta Wannan  Jigo a Jam'iyyar PDP, Segun Sowunmi yace a shirye yake ya koma APC duk da a baya ya soki jam'iyyar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *