
Wata kungiyar yarbawa me suna Ìgbìnmó Májékóbájé Ilé-Yorùbá ta yi kira ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump da ya tursasa malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya kai jami’an tsaro maboyar ‘yan Bindiga.
Kungiyar tace tunda Sheikh Gumi ya iya kai ‘yan jarida da sauransu irin wannan maboya kuma yana kare ‘yan Bindigar, ya kamata a tasa shi gaba ya kai jami’an tsaro maboyarsu.
Shugaban kungiyar, Olusola Badero ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar inda ya bayyana takaici kan yanda ake ganin ‘yan siyasa na yin sulhu da ‘yan Bindigar a Arewa.
Yace ya kamata a kama Sheikh Gumi dan yana da hannu a lamarin.