
Rahotanni sun bayyana cewa a yayin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ke shirin kulla alaka me karfi dan kayar da Tinubu a zaben shekarar 2027, Gwamnonin PDP sun daina daga wayarsu idan sun kirasu.
Wani Jigo a jam’iyyar APC, Ayekooto Akindele ne ya bayyana hakan.
Yace Gwamnonin PDP irinsu Ademola Adeleke basa daukar wayar Atiku da El-Rufai da rana a yanzu.
Yana martanine kan rahoton dake cewa, Gwamnonin PDP din sun hada kai da Tinubu dan bashi goyon baya ya zarce a shekarar 2027.
Ya kara da cewa, Babu yadda Atiku da El-Rufai zasu iya hana Tinubu zama shugaban kasa a shekarar 2027.