WATA SABUWA: An Bankaɗo Cewa Babu Sa Hannun Alƙalin Da Ake Iƙrarin Ya Dakatar Da Naɗin Sarki Sanusi II.
Domin a lokacin ma an ce Mai Shari’a A.M Liman yana Amurka
Kamar yadda fitaccen ɗan jaridar nan Ja’afar Ja’afar ya bayyana a shafin sa ya nuna bambancin dake jikin sa hannun da Jostice A. M. Liman yake yi a duk lokacin da ya yi hukunci da kuma wanda ake yaɗawa yanzu.
Ya ce: Kwatanta sa hannun mai shari’a Liman na yau da kullum, da kuma na dokar da ake amfani da shi yanzu wajen kawo rashin zaman lafiya a Kano ku ga bambancin.
Shin alkali ya canza sa hannun sa ko ya ba wani izini ya canza shi? ~ Cewar Jaafar Jaafar