
Wasu musamman masu goyon bayan Ministan babban Birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike sun fara kiran a kori sojan ruwa da ya tare ya hana Ministan shiga wani fili a Abuja.
Masu kiran dai na ganin abinda sojan yayi ya sabawa dokar kasa da kuma hana hukuma yin abinda ya dace.
Sojan dai ya hana Wike Shiga wani fili ne a Abuja inda yace umarni aka bashi.
Dole Wike ya fasa shiga filin inda ya tafi yana zage-zagi.