
Dan fafutuka kuma Lauya, Deji Adeyanju ya yi zargin cewa, Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da dan takarar shugaban kasa na Labour party, Peter Obi, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu sukawa aiki a shekarar 2023.
Ya bayyana cewa kuma akwai yiyuwar a shekarar 2023 ma zasu sake yi masa.
Deji ya bayyana hakane a shafinsa na X inda yake sharhi game da hadakar ‘yan Adawa da ake shirin kullawa.
Yace idan ana son wannan hadaka ta yi aiki, sai Atiku da Peter Obi sun koma gefe sun bar wanda bai goyon bayan kowa ya jagoranci wannan tafiya.
Deji yace amma da wuya Peter Obi ya yadda a yi wata hadaka dashi